
Mun San Asalin SDP Don Haka Bazata Zama Barazana Garemu Ba - Inji Faruku Inabo
A dai dai lokacin da gwamnatocin jahohi da na tarayya ke dab da cika shekaru biyu kan karagamar mulki, bayanai sun nuna cewa tuni kowane tsuntsu yafara kukan gidan su.
Lamarin siyasa a najeriya dai na bayyana ne a dai dai lokacin da yan siyasa suka fara neman mafaka ta hanyar sauya sheqa daga wata jam’iya zuwa wata jam’iyya.
A jahar kebbi dai wani abu da ya tayar da kura shine wani rahoton da ya nuna cewa gwamnoni akalla 5 na jam’iyar APC ciki harda kauran gwandu na shirin ficewa daga jam’iyar zuwa wata jam’iyar.
Wannan labari dai ya bar baya da qura duk kuwa da irin yanda ake jiyo kauran gwandu na ikirarin cewa bazai fice daga jam’iyyar APC ba.
Akan haka ne gwamna Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya hada hancin kusoshin jam’iyar APC da suka hada kwamishoni, shugabannin kana nan hukumomi mashawarta na musamman da kuma sauran shugabannin hukumomi domnin sheda musu matsayar shi tareda musunta wannan rahoton.
“hakika ina nan daram a cikin jam’iyata ta APC, kuma ina mai sanar daku cewa ba gudu ba ja da baya indai APC ce yanzu aka fara” inji kauran gwandu
A yayin taron dai wakilan hukumomi daban daban ciki harda na hukumar jin dadin alhazzai ta jaha Alhaji Faruku Musa Yaro Inabo sun bayyana goyon bayan su dari bisa dari kan gwamnatin kauran gwandu da kuma ta shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Faruku Inabo yace ba wata maja da zata basu tsoro kuma a shirye suke wajen tabbatarda cewa kauran gwandu da tinubu sun dawo karo na biyu a zaben 2027 mai zuwa.
“Mu munsan asalin SDP don haka babu wata matsala da zata iya kawo muna, jahar kebbi ta kaura ce da tinubu a zaben 2027 da yarda Allah” inji Inabo
“Duk masu son zuwa wata jam’iya wai SDP gasu ga wuri, ko wasu yan adawa daga jam’iyar PDP tuni sukayima kansu kiyamullaili, muna kara jaddada ma al’umma najeriya da jahar kebbi cewa dawowar tinubu da kauran gwandu kamar anyi angama ne”.
Yanzu dai za’a iya cewa kallo ya koma sama domin kuwa al’ummar jahar kebbi sune zasuyi alkanci a zaben 2027 mai zuwa.
Jabir Ridwan