
Yawan marasa aikin yi ya katutu a Afirka ta Kudu
Ɓangaren samar da aikin yi na Afirka ta Kudu na ƙara shiga cikin matsi bayan yawan marasa aikin yi a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 32.9 a cikin ɗari a watanni uku na farkon shekarar 2025.
Yawan marasa aikin yin ya ƙaru ne daga kashi 31.9 cikin ɗari a watanni uku na ƙarshen shekarar 2024 da ta gabata.
Alƙaluma sun nuna cewa a yanzu mutanen da ba su da aikin yi a ƙasar sun kai miliyan takwas ta dubu ɗari biyu da ashirin da takwas (8.228).
Sai dai idan aka faɗaɗa alƙaluman domin haɗawa da waɗanda suka saduda da neman aiki, yawan marasa aikin yi a ƙasar ya ɗaga ne zuwa sama da kashi 43 cikin ɗari.
Ɓangaren da ya fi fama da hasarar guraben aikin yi shi ne ɓangaren kasuwanci da gine-gine, yayin da aka samu ƙarin guraben ayyukan yi a ɓangaren sufuri da harkar kuɗi.