
Tinubu zai Dauki Dubban Matasa Aiki domin Tsaron Dazukan Najeriya
Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kafa jami’an tsaron dazuka domin tinkarar kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya. Wannan mataki ya biyo bayan karuwar hare-hare daga ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da ke fakewa a dazuka suna kai farmaki a jihohi daban-daban.
Tinubu zai Dauki Dubban Matasa Aiki domin Tsaron Dazukan Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa sababbin jami’an tsaron dazuka domin kare jejin Najeriya daga ‘yan ta’adda da miyagu Za a dauki matasa masu yawa aiki a wannan sabon tsarin da gwamnatin tarayya da jihohi ke kokarin aiwatarwa a Najeriya Ma’aikatar Muhalli da Ofishin Mai ba da Shawara kan Tsaro (NSA) za su jagoranci daukar ma’aikatan da kuma aiwatar da tsarin.