Jam iyyar SDP Ta Zo da Sabon Shiri, Ta Saɓawa Atiku da El Rufai kan Kifar da Tinubu a 2027

Yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara kankama a Najeriya, jam'iyyar SDP ta bayyana kwarin gwiwar cewa ita za ta karɓi mulkin ƙasar nan. SDP ta ce tana da ƙwarin gwiwar cewa za ta karbi mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a 2027. 

 

Mataimakin shugaban SDP na kasa a yankin Arewa ta Tsakiya, Abubakar Dogara, ne ya bayyana hakan a taron jam'iyya da aka gudanar a ranar Alhamis a jihar Nasarawa.

 

SDP za ta kwace mulki da ikon Allah' Dogara ya ce jam’iyyar na kokarin fadada yawan mambobinta a fadin kasar nan, yana mai jaddada cewa SDP ta zama abar kauna ga ‘yan Najeriya a halin yanzu. 

 

Abubakar Dogara ya ce: “Muna gudanar da taruka tun daga matakin shiyya, matakin kasa, mazabu, matakin jiha har zuwa kananan hukumomi. “Wannan na daga cikin shiri da muke yi domin karbar mulki a 2027, idan Allah ya yarda. Adadin mambobinmu kullum yana karewa saboda yawan masu shiga jam’iyyar.


Comment As:

Comment (0)