
Jam iyyar SDP Ta Zo da Sabon Shiri, Ta Saɓawa Atiku da El Rufai kan Kifar da Tinubu a 2027
Yayin da shirye-shiryen zaÉ“en 2027 ke Æ™ara kankama a Najeriya, jam'iyyar SDP ta bayyana kwarin gwiwar cewa ita za ta karÉ“i mulkin Æ™asar nan. SDP ta ce tana da Æ™warin gwiwar cewa za ta karbi mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC a zaÉ“en shugaban Æ™asar da za a yi a 2027.Â
Â
Mataimakin shugaban SDP na kasa a yankin Arewa ta Tsakiya, Abubakar Dogara, ne ya bayyana hakan a taron jam'iyya da aka gudanar a ranar Alhamis a jihar Nasarawa.
Â
SDP za ta kwace mulki da ikon Allah' Dogara ya ce jam’iyyar na kokarin fadada yawan mambobinta a fadin kasar nan, yana mai jaddada cewa SDP ta zama abar kauna ga ‘yan Najeriya a halin yanzu.Â
Â
Abubakar Dogara ya ce: “Muna gudanar da taruka tun daga matakin shiyya, matakin kasa, mazabu, matakin jiha har zuwa kananan hukumomi. “Wannan na daga cikin shiri da muke yi domin karbar mulki a 2027, idan Allah ya yarda. Adadin mambobinmu kullum yana karewa saboda yawan masu shiga jam’iyyar.