An Kaddamar da Manhajar Kur ani Mafi Girma a Duniya a Saudiyya

Saudi Arabia - A wani babban mataki na bai wa Alkur’ani girma da muhimmanci a lokacin aikin Hajji, Saudiya ta kaddamar da wani shiri na musamman. Rahotanni sun nuna cewa shirin shi ne mafi girma a duniya dangane da koyar da Alkur’ani mai tsarki.

 

Gulf News ta Rahoto cewa an sanar da kaddamar da shirin ne ta bakin shugaban harkokin addini na Masallacin Harami, Sheikh Dr Abdulrahman bin Abdulaziz Al-Sudais.


 

Shirin zai taimaka wajen kusantar da alhazai da kuma al’ummar Musulmi gaba ɗaya kusa da Alkur’ani mai tsarki ta hanyar karatu, nazari, da kuma kyakkyawan fahimta. Yadda aka tsara shirin Kur'ani a Saudiyya Al-Sudais ya bayyana cewa an tsara shirin cikin manyan hanyoyi da dama, ciki har da tallafa wa da’irar haddar Qur’ani, rubuce-rubucen ilimi, da kuma amfani da manhajojin zamani. 

 

Manhajar na dauke da dandalin zamani na koyar da Alkur’ani da aka tsara bisa turbar shari’a kuma an tabbatar da sahihancinsa.


Comment As:

Comment (0)