
Zaayi Gasar Kwallon Kafa tsakanin masarautu Domin Murnar Cikar Gwamnatin Tarayya da Ta jaha shekara 2 Kan Mulki.
Za'ayi Gasar Kwallon Kafa tsakanin masarautu Domin Murnar Cikar Gwamnatin Tarayya da Ta jaha shekara 2 Kan Mulki.
An qaddamar da kwamitin Gasar kwallon kafa da za'ayi domin murnar Cika Shekaru 2 Kan karagar Mulki GA gwamnan jaha da Dr Nasir Idris Kauran Gwandu da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Kwamishinan ayukka na Jaha alhaji Faruku Abdullahi Umar Muslim shine shugaban kwamitin yayinda babban Sakatare a ma'aikatar lamurran wasanni da matasa ya zamo sakataren Kwamitin.
A yayin jawabi ga manema labarai a cibiyar Yan jarida, kwamishinan ayukka Abdullahi Muslim yace anyi haka ne domin nuna yabawa GA irin kokarin da gwamnan jaha Dr Nasir Idris Kauran Gwandu keyi wajen kawo cigaba a jaha.
Yace Zaa Fara Gasar ne a Ranar 25 GA watan mayun da muke Ciki kuma Gasar zata zamo tsakanin masarautu hudu dake akwai a fadin jaha.
Muslim yace an tanadi kyaututuka daban daban ga Wadanda sukayi hazaka tareda kyauta Mai tsoka ga magobaya da sukafi nuna biyayya.
Daga karshe anyi Kira ga Yan wasa da zasu fafata da kasance masu bin doka da oda domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.