
Yan bindiga sun kashe Manoma 15 a karamar hukumar Danko Wasagu
Ana zargin ‘yan bindiga da kai hari kauyen Waje da ke karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi, inda suka kashe manoma 15 tare da jikkata wasu uku.
Â
Mataimakin gwamna, Sanata Umar Tafida, wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris a ziyarar ta’aziyya ga hakimin Waje, ya nuna alhini game da lamarin.Â
Â
Gwamnati ta kai dauki garin da aka kashe manoma Ya kuma sanar da bayar da tallafi daga gwamnatin jihar domin taimaka wa iyalan wadanda abin ya shafa, inji rahoton Channels TV.Â
Â
Sanata Tafida ya ce wannan tallafi alamar kokarin gwamnati ne wajen sassauta radadin wannan masifa ga dangin mamata da wadanda suka jikkata. Ya kuma tabbatar wa da al’ummar yankin cewa gwamnatin jihar za ta dauki matakan da suka dace wajen magance matsalar tsaro domin manoma su koma gona cikin kwanciyar hankali.Â
Â
Yadda 'yan bindiga ke matsa wa garin Waje Hakimin Waje, Hon. Bala Danbaba, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa ziyarar da kuma tallafin da ya kira da wanda ya zo cikin lokaci kuma mai amfani.Â
Â
Ya bayyana cewa yankin Danko Wasagu na makwabtaka da jihohin Neja, Zamfara da Sokoto, wanda hakan ke sanya su fuskantar hare-hare daga ‘yan ta’adda. Ya roki gwamnati da ta dauki kwararan matakan tsaro domin toshe hanyoyin da maharan ke amfani da su.