
Ku Taimaki Al umma Kamar Yadda Kauran Gwandu Ke taimakon ku: inji shubagaban jam iyar APC
Shugaban jam'iyar APC na Jaha alhaji Abubakar Kana Zuru ya bayyana cewa masu rike da madafun iko yakamata su rika taimakon al'umma kamar Yadda kauran Gwandu ke taimakon su domin Samun nasarar a kowane mataki.
Kana Zuru dai ya bayyana haka ayayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyar da yagudana a dakin taro na masaukin shugaban kasa dake babban Birnin jaha a Ranar Talata.
Yace " maganar gaskiya kaura na iyakar kokari wajen taimakon masu rike da madafun iko saboda haka babu dalilin kin taimakon al'umma tun daga matakin karamar hukuma har izuwa matakin kasa" inji kana Zuru
Yakara da cewa" Siyasa abuce mai Fadi wacce Akan haka Kauran Gwandu ke fafadadata domin amfanuwar al'umma, a don haka lokaci yayi da duk wani mai mukami a wannan gwamnatin ta jaha KO ta tarayya yayi amfani da abinda yake Samu KO yaya ne domin yataimai al'umma SU San cewa ana mulkar SU"
A nashi bangaren gwamnan jaha Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya godewa Allah da ya gwadamishi wannan Rana wacce ya hada Kan dukkan tsohin gwamnoni ukku da suka Mulki jahar Kebbi waje daya, inda yace wannan alamar nasara ce babba.
"Hakika yau mun Kafa Tarihin da babu wata jaha da aka Kafa irin Shi, kuma hakan yatabbatar muna cewa yanzu jahar Kebbi babu adawa, ina Kira ga kowa da kowa da yabada gudumuwa wajen ganin wannan hadin Kan yazama sanadin cigaba GA al'umma Baki daya". Inji Kauran GwanduÂ
Hakama gwamnan jaha Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya qaddamar da sabbin shugabannin kungiyar "Tinubu Kauran Gwandu Two Times" inda shugaban hukumar kulada kogin rima Alhaji Abubakar Gari Malam Shattiman Gwandu ke Zama shugaban kungiyar.
Kauran Gwandu ya bukaci sabbin shugabannin kungiyar da suyi aiki tare da jam'iyar APC domin ganin Kauran Gwandu da Bola Ahmed Tinubu sunyi nasarar a zaben 2027 Mai zuwa.
Da yake jawabi sabon shugaban kungiyar Alhaji Abubakar Gari Malam Shattiman Gwandu Yabayarda tabbacin cewa Zasu Bada gudumuwa wajen ganin ancimma manfar da aka sa agaba musamman ta Samun nasarar a zabe Mai zuwa.
Taron dai ya Samu halarcin duka Yan majasilun dattawa ukku da suka dawo jam'iyar APC daga PDP, da ministan kasafi da tsare tsaren tattalin arziki kuma tsohon gwamnan jaha Alhaji Abubakar Atiku Bagudu, Yan siyasa, kazalika da Sauran mukarraban gwamnati da sauransu.
Jabir Ridwan