An Samu Kuskure, ÆŠan Sanda Ya Kashe Wani ÆŠalibi da ke Rubuta Jarabawar WAEC

Harsashin bindigar wani dan sanda ya hallaka wani ɗalibi mai shirin rubuta jarabawar kammala sakandire ta WAEC a birnin Ibadan, jihar Oyo. 

 

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a kan titin kasuwar Gbagi, lokacin da ɗalibin ke kan babur tare da mahaifinsa, suna hanyarsu zuwa cibiyar jarrabawa. 

Shaidu sun ce wani ɗan sanda da ke bin wasu da ake zargin 'yan damfara ne ya harba bindiga, amma aka samu kuskure ya samu dalibin, inji rahoton Vanguard. 

 

Rahoton ya nuna cewa an garzaya da yaron zuwa asibitin Welfare yayin da jini ke zuba daga jikinsa. Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa bayan isarsu.

 

 Wasu na zargin cewa ɗalibin na tare da ɗan uwansa, wanda kamar tagwaye ne a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata, 20 ga Mayu, 2025. Mutane da dama ciki har da matasa da ƴan kasuwar da ke wajen sun fusata matuka, inda suka ɗauki gawar yaron zuwa ofishin gwamnatin jihar Oyo, tare da yin zanga-zangar neman adalci. Masu zanga-zangar sun bukaci Gwamna Seyi Makinde da yagaggauta daukar mataki, yayin da a hannu daya jami’an tsaro ke ƙoƙarin shawo kan taron jama’ar.

 

'Yan sanda ba su yi martani kan lamarin ba Sai dai jaridar Leadership ta rahoto cewa har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, rundunar Æ´an sandan jihar Oyo ba ta fitar da wata sanarwa ba.

Jabir Ridwan

Comment As:

Comment (0)