
NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Fitaccen Matashi Mai Safarar Kwayoyi, Ya Shiga Hannu.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta gurfanar da wani fitaccen mai safarar kwaya a Kano, Sulaiman Danwawu, a gaban babbar kotun tarayya. A ranar 10 ga Mayu, rundunar ‘yan sandan Kano ta bayyana cafke Sulaiman Danwawu da wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin jihar.
Bayan kama shi, Daily Nigerian ta ruwaito cewa an mika Danwawu ga hukumar NDLEA domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban kotu bisa safarar miyagun kwayoyi.
Zargin da NDLEA ke yi wa Sulaiman Danwawu Rahoton ya ce hukumar NDLEA ta shigar da kara a kotu kan zargin Sulaiman Danwawu mallakar nau’o’in miyagun kwayoyi daban-daban da ba bisa ka’ida ba.
Cikin karar da hukumar ta shigar, an ce: “Kai SULAIMAN AMINU, namiji, mai shekara 37, a ranar 8 ga Mayu, 2025, a titin Cairo, Tudun Yola, karamar hukumar Gwale, Jihar Kano, an kama ka da Tramadol mai nauyin girman 72, wata kwaya da ta yi kama da hodar iblis ba tare da izini ba, wanda hakan laifi ne da ya saba sashi na 19 na dokar NDLEA, Cap N30, Dokokin Tarayyar Najeriya, 2004.”
Hukumar ta NDLEA ta kuma zargi Danwawu da mallakar wasu kwayoyi masu illa da suka hada da giram 1.7 na Rohypnol, kilogiram 24.1 na Pregabalin da sauran miyagun kwayoyi.
A cewar NDLEA, fitaccen matashin yana fuskantar tuhume-tuhume guda takwas – dukkanninsu na da nasaba da safarar miyagun kwayoyi masu hadari da ga jama'a.