Shettima, Atiku, Sarkin Musulmi, Dangote, Manyan Najeriya sun hadu a taron zuba jari a Taraba

Jihar Taraba - Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya isa birnin Jalingo domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron zuba jari da ake gudanarwa a Taraba a bana. Taron na da nufin jawo hankalin masu zuba jari da masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki domin yin hadin gwiwa da jihar. 

 

Tun a kwanakin baya gwamnatin jihar Taraba ta bude shafin yanar gizo domin yin bayani kan lamuran da suka shafi taron. 

 

Taron ya tara manyan ’yan kasuwa, ’yan siyasa da shugabanni daga sassa daban-daban na kasar, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da Sarkin Musulmi. Manyan Najeriya sun je taron tattali a Taraba Taron ya zama wata dama ta musamman wajen nunawa duniya irin albarkatun da jihar Taraba ke da su musamman a fannin noma, makamashi da hakar ma’adanai An bayyana cewa hakan na da tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin Arewa maso Gabas da ma kasa baki daya. 

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da manyan ’yan kasuwa irinsu Alhaji Aliko Dangote da Tony Elumelu sun halarci taron. 

 

Me ake fata a taron tattali na Taraba? An bayyana cewa babban muradin taron shi ne kirkiro hadin gwiwa tsakanin masu zuba jari da jihar domin samar da cigaba da zai dade yana amfani. 

 

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa Taraba na da arzik

i da dama da har yanzu ba a taba amfani da su yadda ya kamata ba, musamman a fannonin noma da makamashi da ma’adanai. 

 

A lokacin taron aka samu halartar wasu gwamnoni irinsu Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago da mataimakin gwamnan Bauchi, da wasu ministoci daga gwamnatin tarayya.


Comment As:

Comment (0)