
Meye zargin da Zulum ya yi wa Yan siyasa da jami an tsaro da sa hannu a rikicin Boko Haram ke nufi?
Masana a Najeriya sun fara tsokaci game da kalaman da Gwamnan jihar Borno ya yi, cewa akwai hannun wasu daga cikin 'yansiyasa da jami'an tsaron kasar wajen tsegunta bayanai da kuma hadin baki da 'yan kungiyar Boko Haram.
Masanan na ganin ya kamata a rika daukar ire-iren wannan zargin da matukar muhimmanci, kuma a bi sawunsa, har gano bakin zaren, domin a magance matsalolin tsaron ta hanyar tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.
Farfesa Babagana Umara Zulum ya furzar da wannan kakkausan zargi ne a wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta News Central.
An ruwaito gwamnan na cewa: ''Ina kuma so in shaida maku, cewa a cikin jami'an tsaro da 'yansiyasa da kuma jama'ar gari akwai masu tsegunta bayanai da hada baki da 'yan kungiyar Boko Haram.
''Abin da ya kamata mu yi a game da hakan, shi ne mu karfafa hanyoyinmu na bayanan sirri, kuma a yi maganin masu aikata hakan ba tare da tausayawa ba.'' In ji shi.
Masana harkar tsaro irin su Dakta Audu Bulama Bukarti, suna ganin wannan zargi da gwamnan ya yi, irin abin nan ne da akan ce, ''Ruwa ba ya tsami banza'':
Â
''Gwamna Zulum dai shi ne gwamnan jihar Borno a yau kuma da yake masu iya magana sun ce mai daki shi ya san inda daki ke masa yoyo za ka yi zaton cewa lalle wannan ba yasasshiyar magana ba ce.
''Lalle gwamnan ya riki wata hujja ce mai karfi da take nuna tabbacin abin da ya yi da'awa kafin ya fito ya yi wannan da'awa, musamman kuma ganin cewa wannan matsala da muke magana kalubale ne mai matukar girma.
'Kuma gwamna ya kwana da sanin cewa irin wannan da'awa tashi za ta tayar da hanakllin mutane saboda haka ina ganin ba zai yi irin wannan magana ba sai yana da hujja.
Saboda haka ina kyautata zaton cewa wani abu shi gwamnan ya gano a cikin su 'yansiyasa da jami'an tsaron da ya yi zargin cewa suna hada kai da 'yan Boko Haram kafin ya fito ya yi wannan magana.''
Masanin tsaron ya yi amanna zargin da gwamnan na jihar Borno ya yi, ba wai shaci fadi ba ne
Dokta Bukarti ya yi tsokaci, cewa bai kamata wannan zargi mai karfi da gwamnan ya yi, ya tsaya a fatar baki kawai ba.
Bakin masana harkar tsaro da dama ya zo daya, a kan cewa matakin bankado masu taimaka wa ruruwar matsalar tsaro, da kuma hukunta su, zai taimaka matuka ga kokarin da ake yi na magance matsalar ta tsaro.