
Gwamnan Jaha Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya biya Naira miliyan 55.81 ga dalibai 61 A Kebbi dake makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya
A kokarin shi na ciyarda bangaren ilmi agaba a wannan jaha gwamnan jaha Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya aminta da biyan kudi kimanin naira miliyan 5.81 makaranta GA dalibban dake karatu a makarantun karatun lauya kimanin SU 61 na Shekarar 2025.
Kowane dalibi dai zai Samu naira dubu 915 domin biyan kudin makaranta da Sauran canjin da zasu rike a hannu domin gudanar da shaanin karatun SU cikin lumana.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wani bayani Mai dauke da sa hannun babba lauyan gwamnatin jaha kuma kwamishinan shariia Dr Junaidu Bello Marshall ya aikewa manema labarai.
Â
A cewar kwamishinan dukkan Wadanda zasu amfana da kudin tuni suka samu kudaden SU Kai tsaye.
Hakama Dr Junaidu ya yabama gwamnan jaha Dr Nasir Idris Kauran Gwandu Kan gudumuwa da yake Baiwa ma'aikatar shari'a
Jabir Ridwan