
Kano: An Cafke Matasa da Ke Bidiyo domin Trending a Kusa da Gidan Gwamnati
Sabon salo na tare manyan hanyoyi a birnin Kano ya dade yana damun al'umma duba yadda ake shiga hakkinsu. Rundunar yan sanda a Kano ta sanar da cafke wasu matasa a kusa da gidan gwamnatin jihar. Kakakin rundunar a Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya tabbatar da haka a yammacin yau Juma'a a shafinsa na Facebook.Â
Â
Kiyawa ya ce matasan da wasu yara sun shiga hannu ne bayan tare hanya a kokarin yin 'trending'. Ya ce lamarin ya faru ne a kan hanya daidai shatale-talen gidan gwamnatin jihar da ke birnin Kano.Â
Â
"An kamo mutume 7 bayan sun tare hanya dai dai shatale-talen Gidan Gwamnatin jihar Kano, suna 'video' domin 'trending.'"