Gwamna Malam Dikko Radda zai tafi hutun sati uku domin kula da lafiyarsa

Gwamna Malam Dikko Radda zai tafi hutun sati uku domin kula da lafiyarsa.

Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD. CON. Ya bayyana aniyar tafiya hutun sati uku, domin kula da lafiyarsa. Hutun wanda zai fara daga ranar 18 ga watan Agusta na 2025.

A Takaice Mataimakin gwamnan jihar Malam Farouk Lawal Jobe zai ci gaba da riƙe jihar har sai Gwamnan ya dawo daga hutun.

Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar Alhaji  Bala Salisu Zango ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren ranar Laraba.

Kawaduws

Comment As:

Comment (0)