An kama matukin babur dauke da ƙuƙunan kan mutane a ogun

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta ce, ta kama wani mai babur mai suna Kadir Owolabi, yana ɗauke da ƙoƙunan kan mutane uku.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Omolola Odutola ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abeokuta ranar Talata.

Odutola ta ce, binciken da jami’an ’yan sandan tafi da gidanka suka yi a jakar wanda ake zargin, ya kai ga gano wasu kan mutane guda uku.

Ta ce, jami’an tsaro ne suka gudanar da aikin bincike na yau da kullum daga rundunar ’yan sanda na tafi da gidanka na 71 PMF, a yankin Awa da ke Ijebu, da ƙarfe 2:00 na rana.

A ranar Litinin, a kan babbar titin Ijebu Ode zuwa Ibadan a mahaɗar ’yan gudun hijira, Oru Ijebu.

“A yayin atisayen, jami’an sun cafke Kadir Owolabi wanda ke kan babur, inda aka gudanar da bincike a kan jakunkunansa, an gano wasu kan mutane guda uku.

“Bincike na farko ya kai ga kama wani wanda ake zargi, mai suna Jamiu Yisa, mai shekara 53, a bayan sakatariyar Ƙaramar hukumar Ijebu Ode,” in ji ta.

Odutola ta ce, Kwamishinan ’yan sanda jihar, Lanre Ogunlowo ya umurci hukumar binciken manyan laifuka ta jihar da ta ɗauki ragamar lamarin domin gudanar da bincike mai zurfi.

Kakakin rundunar ta ƙara da cewa, rundunar ta sake jaddada aniyarta na ɗaukar ƙwararan matakai na yaƙi da miyagun laifuka, ta kuma  buƙaci mazauna yankin da su ba ’yan sanda haɗin kai tare da ba jama’a tabbacin amincewa da su da kuma basu kariyar sirri.

DW

Comment As:

Comment (0)