
Masu garkuwar da mutane sun sace tsohon kansila a jiha katsina
Ƴan bindiga a garin Dayi dake karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina sun yi garkuwa da wani tsohon kansila, bayan wani hari da suka kai a garin a daren jiya Alhamis.
Wani mazaunin garin mai suna Abubakar Ibrahim ya bayyanawa Periom News Hausa cewa ƴanbindigar sun shiga garin ne cikin dare inda suka fara harbi kafin daga baya su kama tsohon kansilan, mai suna Alhaji Nasiru Abdullahi Dayi
“Cikin dare suka shigo muna zazzaune a waje suka fara harbi nan take kowa ya gudu amma daga baya muka samu labarin sun tafi da Nasiru Abdullahi Dayi, tsohon kansila ne” a cewar wani mazaunin garin
Ya ƙara da cewa babu wanda ƴanbindigar suka harba a lokacin da suka kai harin amma dai sun tafi da mutum ɗaya.
Jihar Katsina dai tana ɗaya daga cikin jihohin da suke fama da hare-haren ƴanbindiga a Arewa maso yammacin ƙasar nan.
Periom