
Hukumomin Shari'a sun amince da Naira Dubu 20 a matsayin mafi karancin Sadaki
Hukumomin Shari'a sun amince da Naira Dubu 20 a matsayin mafi karancin Sadaki
Hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar Kano tare da Hukumar Shari’a, Majalisar Malamai, Kungiyar Limaman Masallatan Juma’a da Kungiyar Ma’aikatan Zakka da Wakafi ta Kasa sun amince da sabbin ka’idoji kan Nisabin Zakka, Diyyar Rai da Sadakin Aure a jihar.
A taron da aka gudanar a Kano ranar Alhamis, an yanke shawarar amincewa da naira dubu 20 a matsayin mafi ƙarancin sadakin aure, naira miliyan 150 a matsayin diyya ga wanda aka kashe bisa kuskure, da kuma naira dubu 985 a matsayin nisabin zakka, bisa lissafin farashin Durham.
Babban Sakataren Kungiyar Ma’aikatan Zakka da Wakafi ta Kasa, Farfesa Aliyu Tahiru Muhammad na Jami’ar Bayero Kano ne ya bayyana cewa taron ya kuma amince a ci gaba da gudanar da irin wannan zama duk bayan wata uku domin duba da sabunta wadannan ka’idoji.
Haka kuma, an tsara a sanar da gwamnatin jihar domin shirya taron wayar da kai tare da ‘yan jarida, da kuma isar da sakonni ta hanyoyin da suka dace.
Nagarifmradio