
Hukumomin Tsaro na Najeriya Sun Kama Manyan Shugabannin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ansaru
Hukumomin Tsaro na Najeriya Sun Kama Manyan Shugabannin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ansaru
Hukumomin tsaro na Najeriya sun tabbatar da cafke wasu manyan shugabannin Æ™ungiyar ta’addanci ta Ansaru, wacce ke da alaÆ™a da Æ™ungiyar Al-Qaida. Mai ba wa shugaban Æ™asa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da shugabannin tsaro na Æ™asa suka gudanar a Abuja.Â
Ribadu ya ce wannan nasara ta samu ne sakamakon bincike da dabarun hadin gwiwar jami’an tsaro, domin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a ƙasar.
Daga cikin wadanda aka kama akwai Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Barra, da kuma Abubakar Abba wanda ake kira da Mahmud Al-Nigeri ko Malam Mamuda.Â
Ribadu ya ce cafke wadannan shugabannin na daga cikin manyan nasarorin da gwamnati ke samu wajen ragargazar ƙungiyoyin ta’addanci, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga al’umma.
Sabuwar NIG