
Jami'an tsaro sun kashe yan bindiga a birnin kebbi
Rundunar ‘yan sanda ta ceto wasu mutane biyu da aka sace bayan fafatawa da ‘yan bindiga a yankin Ribah, karamar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi.
Rundunar ‘yan sanda ta ceto wasu mutane biyu da aka sace bayan fafatawa da ‘yan bindiga a yankin Ribah, karamar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi.
Mai magana da yawun rundunar, Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi ranar Asabar.
Abubakar ya ce harin ya faru ne a 15 ga Agusta, lokacin da jami’an ‘yan sanda tare da yan sa kai da maharba suka gwabza da ‘yan bindigar a kusa da garin Dankade na tsawon sa’o’i.
An kubutar da mutane biyu:Â Â
Tukur Bello, dan shekara 26 daga karamar hukumar Augie, Kebbi Â
Isyaka Abubakar, dan shekara 25 daga karamar hukumar Gummi, Jihar Zamfara Â
An sace su ne kwanaki shida da suka gabata yayin da suke kiwon shanu a dajin Gairi, Zamfara.
‘Yan sanda sun ce an kai wadanda aka ceto asibiti domin duba lafiyarsu kafin a mika su ga iyalansu.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kebbi, *Bello Sani*, ya yaba da kwazo da jajircewar *DPO na Ribah* da tawagarsa, yana kuma kira ga sauran DPOs da su dauki irin wannan tsattsauran mataki wajen sintiri da tabbatar da tsaro a tituna da dazuka.
Yankunan Kebbi, Zamfara, Sokoto da Katsina* na fama da matsanancin barazanar ‘yan bindiga, lamarin da ya tilasta wa dubban mutane barin gidajensu.
Nagarifmradio