Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta rage farashin jinyar ciwon ƙoda daga kimanin ₦50,000 zuwa ₦12,000 a Asibitocin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta rage farashin jinyar ciwon ƙoda daga kimanin N50,000 zuwa N12,000 a Asibitocin Tarayya — ragin da ya kai kashi 76 cikin 100.

Wannan saukin farashin ya samu ne bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.

Bwala ya ce hakan zai kawo saukin rayuwa ga dubban ’yan Najeriya da ke fama da cutar, wadda ke bukatar yin jinya sau da dama a kowane mako.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da tallafin tarihi domin rage farashin jinyar ciwon koda ga ’yan Najeriya. An rage farashin kowace wankin ƙoda daga N50,000 zuwa N12,000 kacal, wanda zai kawo sauki ga dubban masu fama da cutar koda,” in ji Bwala.

Sanarwar ta bayyana cewa sabon farashin ya fara aiki a manyan cibiyoyin lafiya guda goma da ke fadin Najeriya, wadanda suka hada da:

Bwala ya kara da cewa, “Za a ƙara wasu cibiyoyin lafiya da asibitocin koyarwa kafin ƙarshen shekara domin faɗaɗa damar a faɗin ƙasa.”

Ya kuma tuna cewa a bara, Shugaba Tinubu ya amince da haihuwa ta hanyar tiyata kyauta ga mata masu juna biyu a asibitocin tarayya — domin inganta lafiyar iyaye mata da rage mace-macen da za a iya kaucewa.

Bwala ya jaddada cewa waɗannan matakai na nuna cikakken kudurin Shugaban Ƙasa na tabbatar da cewa babu ɗan Najeriya da za a hana jinya saboda rashin kuɗi.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)