Ali Nuhu bai rasu ba
Hukumar shirya Finafinai ta Najeriya (NFC) ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa Darakta Janar, Ali Nuhu, ya rasu.
Hukumar shirya Finafinai ta Najeriya (NFC) ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa Darakta Janar, Ali Nuhu, ya rasu.
Jita-jitar ta fara ne bayan wani mai amfani da Facebook mai suna Ifeoma Chigbo ya yada wani bidiyo inda ya yi ikirarin cewa Ali Nuhu ya mutu, Daga bisani kuma, wani rubutu ya sake bayyana cewa shahararren jarumi Mai shirya finafinai ya rasu a wani mummunan haÉ—arin mota.
Sai dai a cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin yada labarai na hukumar, Brian Etuk, ya fitar da yammacin ranar Litinin, NFC ta karyata labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta, tana mai cewa dukkanin jita-jitar ƙarya ce, kuma Kanzon kurege ne, bashi da tushe da Gaskiya.
Nagarifmradio