Matashi ɗan asalin Jihar Kano, Bukhari Sunusi Idris wanda ya wakilci Najeriya a Gasar Karatun Al-ƙur'ani ta Duniya da aka gudanar a Saudiyya ya samu nasarar zuwa mataki na uku, a ɓangaren izu sittin da tafsiri.

Bukhari ya yi wannan nasara ne bayan fafatawa da ’yan takara 128 daga dukkanin ƙasashen Musulmi na duniya.
Hukumomi a Ƙasar Saudiyya sun karrama shi tare samun kyautuka inda ya samu kyautar Riyal ɗin Saudiyya 400,000 wanda ya kai kwatankwacin Naira miliyan 160.
Nagarifmradio