Mafarauci ya kashe mutum 1

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta kama wani maharbi mai shekara 25, Bashir Bala, bisa zargin harbin mutane uku bisa kuskure,

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta kama wani maharbi mai shekara 25, Bashir Bala, bisa zargin harbin mutane uku bisa kuskure, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda, da jikkata 2 a Karamar Hukumar Malumfashi.

Lamarin ya afku ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4:10 na yamma a Marabar Kankara, yankin da ke fama da matsalar tsaro a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa Bala, wanda ke aiki tare da wata tawagar tsaro ta gari, ya je wurin domin siyan wiwi. Sai dai aka samu husuma tsakaninsa da wasu, inda cikin rikicin ya harba bindiga, lamarin da ya rutsa da mutanen.

Katsina

Comment As:

Comment (0)