Alkalai Da Dama Sun Shiga Cikin Siyasa Da Cin Hanci Da Rashawa - Obasanjo

Alkalai Da Dama Sun Shiga Cikin Siyasa Da Cin Hanci Da Rashawa - Obasanjo 

Tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, a ranar Juma’a ya bayyana damuwarsa kan halin da ya ce tsarin shari’ar Najeriya ya shiga.

Obasanjo ya yi nuni da cewa alkalai da dama sun shiga cikin siyasa da cin hanci, abin da ke sa jama’a rasa amana ga kotuna. A cewarsa, “idan alƙalai suka zama marasa tsari, gaskiya da adalci za su zama ruwan dare.”

Ya ƙara da cewa lamarin na barazana ga makomar ƙasar, domin idan shari’a ta lalace, babu abin da zai iya tsaida rugujewar doka da oda.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)