Sokoto zuwa Kebbi

NEMA ta gargadi mazauna Kebbi, Neja da Kwara su bar wuraren da ambaliya ke yawan faruwa

NEMA ta gargadi mazauna Kebbi, Neja da Kwara su bar wuraren da ambaliya ke yawan faruwa

Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta fitar da gaggawar gargadi ga mazauna yankunan da ke bakin Kogin Neja a jihohin Kebbi, Neja da Kwara, tana shawartar su da su bar wuraren su koma inda ya fi aminci, sakamakon karin ruwa da ke kwarara daga Jamhuriyar Benin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a ranar Asabar a Abuja, Daraktar Janar ta NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta bayyana cewa hukumar ta fara aiwatar da matakan shirye-shiryen rigakafi da martani kan ambaliya.

Ta umarci ofisoshin NEMA na shiyya da na yanki da ke kusa da Kogin Neja da su kara kaimi wajen fadakar da jama’a da kuma wayar da kan al’umma a yankunan da ke fuskantar hadarin ambaliya.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)