Jihar Kebbi

YAN SANDA SUN CIMMA NASARA TA KUMA TA CETO WANI DA AKA SACE A KAUYEN KESAN NA KARAMAR HUKUMAR SHANGA

‘YAN SANDA SUN CIMMA NASARA TA KUMA TA CETO WANI DA AKA SACE A KAUYEN KESAN NA KARAMAR HUKUMAR SHANGA

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya wadda ke da alhakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, a ranar 23 ga watan Agusta, 2025 da misalin karfe 5:00 na asuba, wasu gungun masu garkuwa da mutane dauke da makamai sun kai hari a kauyen Kesan da ke karamar hukumar Shanga ta Jihar Kebbi, inda suka sace wani matashi mai suna Abdulmumini Alhaji Ahmadu, namiji, mai shekaru 25.

Da samun rahoton lamarin, DPO na Shanga ya hanzarta tara jami’an ‘yan sanda da vigilante, inda suka bi sahun masu garkuwar kuma suka ceto wanda aka sace. A yayin aikin ceto, masu laifin sun harbi wanda aka sace a kafarsa ta hagu, wanda hakan ya jawo masa rauni mai tsanani sannan suka tsere da shi cikin daji. Jami’an tsaro sun garzaya da shi zuwa asibiti domin jinya, kuma yana samun sauki a halin yanzu.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya sake jaddada kudurin rundunar wajen yaki da miyagun laifuka a fadin jihar domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)