
‘Yan bindiga sun kai hari a Dandume, mutum ɗaya ya rasa ransa
‘Yan bindiga sun kai hari a Dandume, mutum ɗaya ya rasa ransa
A daren Lahadi, 24 ga watan Agusta 2025, ‘yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Dandume da ke jihar Katsina.
Shaidu sun ce maharan sun harbi mutane uku, inda wani matashi mai suna Musbahu Hadi Alhassan ya rasu, sauran biyun kuma ke samun kulawa a asibiti.
Harin ya faru ne cikin daren nan, daidai lokacin da jama’a ke shirin shiga gobe Litinin.
Zuwa yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba.
Nagarifmradio