Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa (NDLEA) a reshen Kano ta ce ta kama wani matashi mai shekaru 29, Adamu Yusuf, da kwayoyin Tramadol 7,000.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa (NDLEA) a reshen Kano ta ce ta kama wani matashi mai shekaru 29, Adamu Yusuf, da kwayoyin Tramadol 7,000.
sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar a ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025 a Kano.
Sanarwar ta ce jami’an ofishin NDLEA da ke Kiru ne suka cafke wanda ake zargin a ranar 23 ga Agusta a kan titin Zaria zuwa Kano, kusa da Kwanar Dangora, yayin da yake dawowa daga Legas dauke da maganin da aka boye a cikin jarkar mai lita 20.
Kwamandan hukumar a Kano, ACGN A.I. Ahmad, ya yaba da aikin da jami’an suka gudanar tare da gode wa shugaban hukumar na ƙasa, Brig. Janar Buba Marwa (mai ritaya), bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike tare da jajircewa wajen yaki da fataucin miyagun ƙwayoyi a Kano
Nagarifmradio