Jirgin daga Abuja zuwa kaduna

Fasinjojin da ke cikin jirgin kasa da ke jigila daga Kaduna zuwa Abuja sun tsallaka rijiya da baya bayan da da ya yi hatsari da su a safiyar Talata.

Fasinjojin da ke cikin jirgin kasa da ke jigila daga Kaduna zuwa Abuja sun tsallaka rijiya da baya bayan da da ya yi hatsari da su a safiyar Talata.

Wani daga cikin fasinjan da ke cikin jirgin kasan ya bayyana cewa jirgin ya sauka daga kan layin dogo, lamarin da ya sa wasu daga cikin taragonsa mirginawa.

Kawo yanzu dai babu bayanai game da musabbabin hatsarin jirgin kasan, ko mutanen da suka samu rauni da makamantansu..

Layin jirin kasa na Kaduna zuwa Abuja, wanda ke da yawan zirga-zirga na yawan fama da matsloli irin haka a ‘yan shekarun nan.

Idan ba a manta ba a makonnin da suka gabata ne Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da cewa kafar daya daga cikin taragon jiragen kasan ya samu matsala a kan layin Kaduna zuwa Abuja.

Kakakin hukumar, Callistun Unyimadu ya tababtar cewa hukumar ta fara daukar matakan shawo kana matsalar, wanda ta ce zai iya shafar yawan jigilar fasinjoji kafin daga bisani komai ya daidaita.

A kan layin ne kuma ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da gomman fasinjoji a watan Maris na shekarar 2022.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)