Ribadu Ya Mika Mutane 128 da Aka Ceto a Zamfara Daga Yan Bindiga Ga Iyalansu Tare da Alwashin Kawo Ƙarshen Ta’addanci.

Ribadu Ya Mika Mutane 128 da Aka Ceto a Zamfara Daga Yan Bindiga Ga Iyalansu Tare da Alwashin Kawo Ƙarshen Ta’addanci. 

Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Kasa (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta tsaya ba wajen fatattakar ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane har sai an kawar da su baki ɗaya. 

Ribadu ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin da ya mika mutane 128 da aka ceto daga hannun ’yan bindiga a Kaura Namoda, Jihar Zamfara. 

“Ba za mu bar wata mafaka ga masu tayar da hankalin ’yan kasa ba. Za mu rutsa su, mu kamo su, kuma mu tabbatar da an gurfanar da su a gaban shari’a.” Inji Ribadu

A nasa jawabin, babban jami’in cibiyar yaƙi da ta’addanci ta kasa (NCTC), Manjo-Janar Adamu Laka, ya bayyana cewa an ceto mutanen a rukunai biyu bayan shirye-shiryen tsaro na hadin gwiwa. Ya ce rukuni na farko da aka ceto ranar 14 ga watan Agusta ya kunshi mutane 42, ciki har da jarirai, yayin da rukuni na biyu da aka kubutar ranar 19 ga watan Agusta ya kunshi mutane 88, inda aka rasa jariri guda sakamakon rashin lafiya da kuma tsananin wahala a sansanin ’yan ta’adda. 

Ya kara da cewa an bai wa wadanda aka ceto kulawar likitoci kafin mika su ga iyalansu.

Ƙaramin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Tanko Sununu, ya yaba wa kokarin jami’an tsaro da gwamnati wajen ceto mutanen. Ya shawarci wadanda aka ceto da su dauki wannan dama a matsayin sabon gini ga rayuwarsu, musamman ta hanyar ilimi. 

Daya daga cikin wadanda aka kubutar, Abdullahi Salisu, ya ce sun kwashe kwanaki 42 a hannun ’yan ta’adda ba tare da abinci ba, kuma ya gode wa Allah da gwamnati bisa nasarar ceto su.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)