
Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa.
’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa.
Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare.
Maharan sun shiga yankin ne ta ɓangaren Katsina ɗauke da bindigogi, inda suka dinga harbi a sama.
Sun harbe wani mutum mai suna Aminu Shehu har lahira, sannan suka yi awon gaba da wani É—an kasuwa mai suna Alhaji Shehu Dakin.
Majiyoyi, sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da wayar Alhaji Shehu wajen kiran iyalansa, inda suka nemi kuÉ—in fansa Naira Miliyan 100.
Wasu mazauna yankin sun ce wannan hari ya tayar musu da hankali tare da sanya su cikin fargaba.
Sun roƙi gwamnati da hukumomin tsaro su kai musu ɗauki cikin gaggawa.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ci tura, domin ba ya ɗaukar waya har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Nagarifmradio