Tsohon sanata mai wakiltar Mazabar Yammacin Kogi, Dino Melaye, an gurfanar da shi a gaban Kotun Majistire ta Babban Birnin Tarayya (FCT) bisa zargin kin biyan harajin samun kudin shiga da ya wuce N509.6m

Tsohon sanata mai wakiltar Mazabar Yammacin Kogi, Dino Melaye, an gurfanar da shi a gaban Kotun Majistire ta Babban Birnin Tarayya (FCT) bisa zargin kin biyan harajin samun kudin shiga da ya wuce N509.6m.

A cewar bayanan kotu, an ce Melaye ya gaza biyan harajin da wajibi ne a kansa na shekarun 2023 da 2024, wanda ya kai N234,896,000 da N274,712,000 bi da bi, kamar yadda Hukumar Haraji ta Babban Birnin Tarayya (FCT-IRS) ta tantance. Jimillar ta kai N509,608,000.00.

Baya ga kin biyan na shekarun 2023 da 2024, FCT-IRS ta kuma zarge shi da biyan ƙasa da kima a harajin shekarun 2020, 2021, da 2022.

Rahotanni sun nuna cewa yayin da Melaye ya bayyana samun kudin shiga na N1,383,334 a 2020, N1,550,000 a 2021, da N6,541,666.67 a 2022, ya biya kawai N100,000.08 a 2020, N120,000 a 2021, da N1,000,000 a 2022. A shekarar 2019, lokacin da yake majalisa, ya bayyana samun N1,258,334 amma ya biya N85,000.08 kacal a matsayin haraji.

An fitar da takardar ƙara ta laifin a ranar 21 ga Agusta, 2025, wadda ta wajabta zuwan sa gaban Kotun Majistire dake Wuse Zone II, Abuja, a ranar 5 ga Satumba, 2025.

Hukumar harajin ta bayyana cewa ta gudanar da bincike kan abin da Melaye yake bi na shekarun 2023 da 2024, amma bayan ya gaza mayar da martani cikin kwanaki 30, sai ta fitar da sanarwar “best judgment assessment” a ranar 23 ga Yuni, 2025.

Sanarwar ta kuma makala a gidan Melaye dake Maitama a ranar 9 ga Yuli, 2025, bayan an zarge shi da kauce wa karɓar takarda.

FCT-IRS ta ce: “Duk da tunatarwa da lokaci mai yawa da aka bashi, kin bin dokar Sashe na 41 na Dokar Harajin Samun Kudin Shiga ta 2011 laifi ne. Saboda haka, bisa Sashe na 54(3), hukumar ta ɗauki matakin tantance harajin da ya wajaba bisa mafi dacewa.”

Hukuncin da ka iya fuskanta idan aka same shi da laifi

Bisa ga Dokar Harajin Samun Kudin Shiga ta 2011 (PITA), kin bayyana haraji, rage yawan kudin shiga da ainihi, ko kauce wa biyan haraji gaba ɗaya, na iya jawo tara mai tsanani da kuma dawo da kudaden da ba a biya ba. Bugu da ƙari, ana iya ɗaukar matakan shari’ar laifi a kansa.

Idan FCT-IRS ta ci nasara a shari’ar, Melaye ba kawai zai biya N509.6m na 2023 da 2024 ba ne, amma har da karin bashin haraji na 2020–2022, tara, da kudin ruwa wanda zai iya ƙara girma fiye da hakan. Kamar yadda Premium Times ta Rawaito.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)