
DSS da Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 50, sun ceto waɗanda aka sace a jihar Niger
DSS da Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 50, sun ceto waÉ—anda aka sace a jihar NigerÂ
Rundunar DSS tare da Sojojin Najeriya sun yi babban nasara a jihar Neja, inda suka kashe sama da ‘yan bindiga 50 tare da ceto mutanen da aka sace a ƙauyen Kumbashi, karamar hukumar Mariga, a ranar Talata 26 ga Agusta.
Shaidu sun ce kusan ‘yan bindiga 300 dauke da manyan makamai suka kai hari da misalin ƙarfe 3 na rana, inda suka nufi sansanin DSS da ke yankin. Sai dai jami’an tsaro sun yi musu luguden wuta, suka fatattake su, inda wasu da dama suka tsere da rauni
Nagarifmradio