Wani jami’in ’yan sandan MOPOL mai mukamin Insfekta ya harbe wani soja har lahira a garin Futuk na karamar hukumar Alkaleri a Bauchi.
Wani jami’in ’yan sandan MOPOL mai mukamin Insfekta ya harbe wani soja har lahira a garin Futuk na karamar hukumar Alkaleri a Bauchi.
Â
Lamarin ya faru ne bayan takaddama kan wata mota dauke da ma’adinai da ake zargin an hako ba bisa ka’ida ba.Â
Â
Rahotanni sun ce dan sandan da ake zargin yana rakiyar motar ne.
Â
An cafke dan sandan tare da bindigarsa yayin da direban motar ya tsere.Â
Â
To saidai sojan da aka harba ya rasu bayan an garzaya da shi asibiti a Gombe.
Nagarifmradio