Majalisar Zartarwa ta Jihar Sokoto ta Amince da Ayyuka Masu Muhimmanci

Majalisar Zartarwa ta Jihar Sokoto ta Amince da Ayyuka Masu Muhimmanci

 

Majalisar zartarwa ta jihar Sokoto ta amince da aiwatar da wasu manyan ayyuka masu muhimmanci, wadanda suka haÉ—a da gyaran asibitoci tara, ci gaba da gina manyan hanyoyi, da kuma kafa cibiyar kula da kiwon dabbobi.

 

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Faruk Umar Wurno, ya bayyana cewa an bayar da kwangilar gyaran asibitoci tara, tare da sanya wa’adin kammalawa cikin watanni shida. Ya kuma jaddada cewa duk wanda ya jinkirta aikin zai fuskanci hukunci.

 

Asibitocin da za a gyara sun haɗa da:  

- Babbar Asibitin Silame  

- Asibitin Wamakko  

- Asibitin Binji  

- Asibitin Kware  

- Asibitin Gwadabawa  

- Asibitin Goronyo  

- Asibitin Illela  

 

Dakta Wurno ya ƙara da cewa kudin da aka ware wa Asibitin Illela ya fi na sauran, kasancewar aikin ya haɗa da gyare-gyare, sake gina bangaren da gobara ta lalata, da kuma kammala wani gini da aka bari a baya.

 

---

 

*Kiran Noma da Bin Shawarwarin Masana*

 

An yi kira ga manoma da su nemi shawarwari daga masana kafin su fara noma ko girbi, domin kaucewa asarar amfanin gona sakamakon ambaliyar ruwa.

 

Wannan kiran ya fito ne daga Yahaya Sa’idu Isa, Mataimakin Shugaban Sashen Karatu a Kwalejin Koyon Aikin Gona da Kiwo da ke Wurno, a lokacin wata hira.

 

Ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta zama barazana ga manoma a bana, don haka akwai bukatar su nemi shawarwari daga kwararru kan dabarun noma na zamani, wadanda za su kare gonaki daga ambaliya, tare da ƙara yawan amfanin gona.

 

A cewarsa, bin wadannan shawarwari zai taimaka wajen rage asara, bunkasa samar da abinci, da kuma inganta tattalin arzikin manoma.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)