Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 14, karkashin Mai Shari’a Maryam Sabo, ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 21 ga wani malamin makarantar Islamiyya mai suna Nasif Shu’aibu, bisa samun sa da laifin yi wa ɗalibarsa ƴar shekara 9 fyade.

Arewa Updates ta rawaito cewa, yayin zaman kotun Lauya mai gabatar da ƙara, Barista Fa’iza Dahiru Sidi, ta gabatar da shaidu guda biyar a gaban kotu, yayin da lauyan wanda ake ƙara Barista Aminu Umar ya gabatar da shaida guda ɗaya.
Kotun ta bayyana cewa shaidu sun tabbatar masa da laifin, inda ta yanke hukuncin É—aurin shekaru 14 a gidan yari kan laifin fyade da kuma shekaru 7 kan laifin lalata yarinya.
Haka zalika, kotun ta umarci wanda aka yanke wa hukuncin ya biya tarar naira 200,000 tare da diyya ga yarinyar da abin ya shafa ta naira 50,000.
An kama malamin ne tun shekarar 2022 bisa zargin haike mata, lokacin da ya ke koyar da yarinyar a makarantar Islamiyya da ke Unguwar Mariri, a ƙaramar hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.
Nagarifmradio