Karamar hukumar Kurfi a Jihar Katsina tayi sasanci da yan Bindigar da su ka addabi karamar hukumar.

Karamar hukumar Kurfi a Jihar Katsina tayi sasanci da 'yan Bindigar da su ka addabi karamar hukumar. 

Maradin Katsina Hakimin Kurfi Alhaji Mansur Amadu Kurfi da Shugaban karamar hukumar Kurfi Hon. Babangida Abdullahi Kurfi su ka Jagoranci sasanci da 'yan Bindiga da su ka addabi karamar hukumar domin maslaha da zaman lafiyar Al'ummar yankin. 

Karamar hukumar Kurfi tana cikin kananan hukumomin da matsalar tsaro tayi kamari a Jihar Katsina, wanda hakan ya kawo cikas ga harkokin Al'umma na yau da kullum a yankin. 

Tun da farko da yake gabatar da jawabinsa, Maradin Katsina Hakimin Kurfi Alhaji Mansur Amadu Kurfi ya nuna jin dadinshi akan wannan sasanci da akayi domin maslahar Al'umma, ya kuma yi alkawalin rike amana ta Fulanin tare da basu umurnin su kawo wasu daga cikinsu da nada su shugabannin su na gargajiya. 

Shugabannin Fulanin Dajin da su ka gabatar da jawabai a wurin taron sasancin sun hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga, Sani Muhindinge, Yahaya Sani (Hayyu), da Alhaji Shu'aibu. 

Sun bayyana cikakken goyon bayansu akan wannan sasanci da akayi tare da daukar alkawalin daina kai hare, hare, da kashe, kashe, da satar mutane don neman kudin fansa, gami da satar shanu, a yankin karamar hukumar Kurfi da kewaye, manoma su ci gaba da harkokin nomansu cikin walwala ba tare da wata fargaba ba. 

Daga karshe sunyi kira da sako masu mutanen su dake tsare, kuma suma daga yau zasuje su sako mutanen dake wurinsu wadanda sukayi garkuwa dasu, kowa ya koma gidanshi, zaman lafiya ya samu a karamar hukumar Kurfi babu sauran wani tashin hankali sun dauki alkawali. 

Shima a nashi jawabin, shugaban karamar hukumar Kurfi Hon. Babangida Abdullahi Kurfi ya bayyana farin cikinsa mara musaltuwa a wannan rana na kawo karshen matsalar tsaro a karamar hukumar Kurfi, sannan ya yi alkawalin cika duk bukatun da Fulanin Dajin su ka nema.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)