
Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu, ya kaddamar da shirin dasa itatuwa na shekarar 2025 a garin Sabon Birni Kasarawa, inda ya bukaci al umma da su hada hannu wajen dakile yaduwar hamada a fadin jihar.
Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu, ya kaddamar da shirin dasa itatuwa na shekarar 2025 a garin Sabon Birni Kasarawa, inda ya bukaci al umma da su hada hannu wajen dakile yaduwar hamada a fadin jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samu dimbin tsirrai na muhalli da kuma na kasuwanci ta hannun ma’aikatar muhalli domin rabawa kananan hukumomi 23 na jihar, tare da umartar shugabanninsu da su tabbatar da shuka tsirran a yankunansu cikin gaggawa.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin wayar da kai kan illar sare itatuwa ba tare da tsari ba, yana mai cewa duk inda aka sare itace wajibi ne a dasa sabon.Â
Ya kara da cewa a matsayin musulmi, dasa itatuwa ibada ce ta sadaqatul jariya wadda lada ke ci gaba bayan mutuwa.
Haka kuma, ya godewa hukumar Great Green Wall bisa rabawa jihar tsirran dabino guda dubu dari hudu da hamsin, wadanda za a rarraba a cibiyoyin kiwo da aka tanada a Gundunga, Goronyo da Sanyinna, domin rabawa jama’a, kungiyoyi, makarantun gwamnati da wuraren ibada.
Gwamnan ya kuma yaba wa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa tallafa wa shirin Great Green Wall da ke yaki da dumamar yanayi, yaduwar hamada da sauran matsalolin muhalli.Â
A nasa jawabin, kwamishinan muhalli na jihar, Hon. Nura Shehu Tangaza, ya ce gwamnatin ta sanya aniyar dasa tsirrai dubu dari biyar a wannan shekara tare da hadin kan al’umma.
Nagarifmradio