
Gurfanar da Jaafar Jaafar a Kotu Saboda Ya Binciko Badakalar N6.5B Ya Nuna Gwamnatin Kano Ta Gaza Inji Lauya Abba Hikima
Gurfanar da Jaafar Jaafar a Kotu Saboda Ya Binciko Badakalar N6.5B Ya Nuna Gwamnatin Kano Ta Gaza Inji Lauya Abba Hikima
Fitaccen ɗan jarida, Ja’afar Ja’afar, Zai gurfana a gaban kotu bisa tuhumar wallafa rahoton badakalar naira biliyan 6.5 da ake zargin Protocol na Gwamnan Jihar Kano. Abba Rogo
Tuhumar ta haifar da cece-kuce a fagen siyasa da al’umma, inda lauyoyi da masu rajin kare hakkin bil’adama suka bayyana damuwarsu kan yadda ake amfani da kotu wajen tsoratar da ‘yan jarida.
Barista Abba Hikima Fagge, shahararren lauya kuma mai kare hakkin bil’adama, ya bayyana cewa gurfanar da Ja’afar ba wai kawai batu ne na shari’a ba, illa kuwa ya fito fili ya nuna irin lalacewar tsarin mulki da gwamnatin Kano ta fada ciki.
“Idan gwamnati ta mayar da kotu makamin murkushe gaskiya, to wannan alama ce ta gazawa da lalacewar shugabanci. Abin da ake yi wa Ja’afar Ja’afar ba wai shari’a ba ce, illa dai yunƙurin rufe bakin gaskiya da hana al’umma jin abin da ke faruwa,” in ji shi.