
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta bayyana cewa dukkan jami’o’in gwamnati kusan 150 da ke ƙarƙashin kulawar ta na iya shiga yajin aiki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Wannan lamari ya biyo bayan da gwamnati ta musanta cewa ta rattaba h
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta bayyana cewa dukkan jami’o’in gwamnati kusan 150 da ke ƙarƙashin kulawar ta na iya shiga yajin aiki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wannan lamari ya biyo bayan da gwamnati ta musanta cewa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ASUU, inda ta bayyana takardun da ƙungiyar ke magana a kansu a matsayin shawarwari ne kawai.
Daga ranar Litinin din wannan makon, rassan ASUU daban-daban sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ƙungiyar ko kuma a fuskanci yajin aikin da zai shafi ɗalibai kusan miliyan biyu a faɗin ƙasa.
Manyan matsalolin sun haɗa da rashin biyan albashin watanni uku da rabi da aka hana da rashin biyan cikon kuɗin albashi na ƙarin matsayi da rashin sakin kuɗaɗen inganta jami’o’i da sauya sunan Jami’ar Maiduguri, da batun kudin ritaya ga malaman jami’a.
hakama asuu ta bukaci inganta albashin mambobin ta baiwa jami'o'i kudade isassu da yancin gashin kai tareda yin bitar dokokin gudanarwar hukumar kulada jami'o'i da kuma na hukumar zana jarabawar share fagen shiga jami'a waton jamb da sauransu
daga karshe shugaban kungiyar farfesa chris piwuna yace kalaman ministan sun nuna cewa gwamnati bata ajiye bayanai yanda yakamata.