Sakamakon bincike kan ayyukan gwamnatin Nijeriya da ake cigaba da gunarwa na nuna cewa shugaba Tinubu ya karkata kaso mafi rinjaye wurin yi wa jihar Legas aiki da sauran jihohin Kurmi.

 Sakamakon bincike kan ayyukan gwamnatin Nijeriya da ake cigaba da gunarwa na nuna cewa shugaba Tinubu ya karkata kaso mafi rinjaye wurin yi wa jihar Legas aiki da sauran jihohin Kurmi. 

Kawo yanzu, an gano cewa gwamnatin Tinubu ta kashe Naira Tiriliyan 3.9 wurin yi wa Legas aiki, kuÉ—in da ya ninka abin da ya kashe wa sauran sassan Nijeriya sau 111 a cikin shekaru biyu.

Wani bincike da kafar yaÉ—a labarai ta Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa Majalisar Zartarwa Ta Nijeriya (FEC) ta amince a kashe Naira tiriliyan 5.97 a Kudu maso Yammacin Nijeriya, yayin da ta amince a kashe Naira tiriliyan 2.41 a Kudu maso Kudu, sai kuma aka ware Naira biliyan 407.49 a Kudu maso Gabas.

Rahoton ya ce, an ware Naira tiriliyan 1.15 domin jihohin Arewa ta Tsakiyar Nijeriyar (Ciki har da Abuja) sai Arewa maso Yamma, inda aka ware Naira Tiriliyan 2.7, yayin da aka ware Naira biliyan 403.98. 

Daga cikin gagaruman ayyukan da gwamnatin Tinubu ta bada umurnin yi a jihar Legas da ya ɗauki hankalin sauran ‘yan sassan jihohin shine ware Naira biliyan 712 domin zamanantar da filin tashi da sauƙar jiragen sama na ƙasa da ƙasa Murtala Muhammed dake Legas.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)