Sama da Daliban Najeriya 396,000 ne suka ci gajiyar Tallafin Karatun Gwamnatin Tarayya na NELFUND

Sama da Daliban Najeriya 396,000 ne suka ci gajiyar Tallafin Karatun Gwamnatin Tarayya na NELFUND

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sama da dalibai 396,000 a fadin ƙasar nan sun ci gajiyar tallafin biyan kuɗin makaranta na NELFUND tun daga lokacin da aka fara aiwatar da shi ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu. Wannan bayani ya fito ne daga bakin wakilin Ministan Yaɗa Labarai da wayar da kam Jama’a, Malam Lawal Shuaibu, a wani taron tattaunawa da aka gudanar a Lokoja. 

Ya ce shirin ya sauƙaƙa wa ɗalibai da iyayensu wahalhalun kashe kudi, tare da tabbatar da cewa ba a katse wa ɗalibai karatu ba saboda rashin kuɗin makaranta.

Shuaibu ya jaddada cewa NELFUND ya kawo sauyi ga rayuwar ɗalibai da dama, inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da faɗaɗa shirin domin tabbatar da cewa duk wanda ke da burin karatu ya samu damar cimma hakan. 

Ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin ginshiƙi na samar da makoma mai kyau ga matasa da kuma taimaka musu wajen cika burinsu na ilimi.

Mai Martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Ibrahim Gambo, wanda ya samu wakilci a wajen taron, ya yaba wa shirin NELFUND, inda ya ce ya sauƙaƙa wa iyaye da ɗalibai nauyin kuɗin makaranta da kuma tsadar rayuwa. 

Ya yi kira da a faɗaɗa irin wannan tallafi har zuwa matakin ƙauyuka domin ƙarin ɗalibai da zasu amfana, yana mai cewa wannan tsari yana da matuƙar tasiri wajen samar da ilimi mai dorewa a ƙasar.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)