
Duk da waɗannan hujjoji da ake bayyana, gwamnatin Kano ta fito ta kare hadimin gwamnan tana mai watsi da rahoton zargin satar Naira biliyan 6.5
Duk da waɗannan hujjoji da ake bayyana, gwamnatin Kano ta fito ta kare hadimin gwamnan tana mai watsi da rahoton zargin satar Naira biliyan 6.5 da cewa ƙarya ake yi kuma ‘yan adawa ne suka ɗauki nauyin wannan domin ɓata wa gwamnatin Abba suna.
Gwamnatin ta kuma kafe kan cewa kowacce ma’aikata da hukuma da cibiyoyin gwamnati suna kashe kuɗinsu yadda ya kamata (yadda aka kasafta musu), tana mai cewa ba wani jami’in gwamnati da ke da ikon taɓa ko taro da sisi.
Sannan ta ce daraktan tsare-tsaren ne ke kula da harkar sufuri da walwala da wurin kwana da tafiye-tafiyen gwamnan a ciki da wajen Najeriya da ma taimaka wa manyan baki da suka haɗa da shugaban ƙasa da ministoci da jakadu da sauransu.
Sai dai duk da wannan iƙirari da gwamnatin Kano ta yi, EFCC da ICPC suna cigaba bincike kan wannan badaƙala.
Masu binciken sun ce cikin makonni masu zuwa za su ƙara bankaɗo wasu abubuwa da za su tabbatar da Rogo a matsayin ɗaya daga cikin “ɓarayin gwamnati” da ba a taɓa yin kamarsu ba a tarihi.
Nagarifmradio