Tsohon Ministan Shari a na Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya yi zargin cewa farmakin da aka kai wa tawagarsa a lokacin da suka je ziyarar ta’aziyya a Birnin Kebbi bai kasance abin bazata ba, illa dai an aikata shi da sanin jam’iyyar APC ta jihar Kebbi.

Tsohon Ministan Shari a na Tarayya Abubakar Malami (SAN)  ya yi zargin cewa farmakin da aka kai wa tawagarsa a lokacin da suka je ziyarar ta’aziyya a Birnin Kebbi bai kasance abin bazata ba, illa dai an aikata shi da sanin jam’iyyar APC ta jihar Kebbi.

Malami, wanda shi ne jigo a jam’iyyar ADC a halin yanzu, ya bayyana cewa motoci masu yawa daga cikin jerin gwanon tawagarsa an farfasa su yayin wannan farmaki, abin da ya kira da “mugun aiki” da ya saba wa al’ada da mutunci.

Ya ce, “Wannan hari da aka kai wa tawagata ba zai yiwu a ce an yi shi ba tare da sanin shugabancin jam’iyyar APC ta jihar Kebbi ba. Mun je wajen Ta'aziyya ne amma aka juya abin zuwa tashin hankali.”

Tsohon Ministan ya kuma bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da gaskiya tare da hukunta masu hannu a cikin wannan al’amari.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)