Hukumar Kula da Gudanar da Ruwa ta Kasa (NIHSA) ta yi hasashen ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 107 na jihohi 21 a fadin Najeriya

Hukumar Kula da Gudanar da Ruwa ta Kasa (NIHSA) ta yi hasashen ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 107 na jihohi 21 a fadin Najeriya tare da gargadin daukar matakin da ya dace.

Daraktan hukumar, Umar Muhammad ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja ranar Litinin, inda ya bayyana cewa ambaliyar za ta iya shafar unguwanni 631 daga ranar 1 zuwa 15 ga watan Satumba na wannan shekarar.

A cikin jihohin da abin zai iya shafa akwai Jigawa da Kaduna da Sokoto da Zamfara da Kebbi da Bauchi da Gombe da Yobe da Nasarawa da Filato da Kogi da Kwara da Legas da Ogun da Ondo da Ribas, da kuma Karin wasu yankuna da dama.

Daraktan ya jaddada muhimmancin shirye-shiryen gaggawa, sannan ya bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma na kananan hukumomi su samar da tsare-tsaren rage munin illar ambaliyar ruwan tare da tanadar da kayan tallafi ga mutanen da abin zai iya shafa.

Hukumar NIHSA ta kuma nemi hadin kan hukumomin tsaro da na lafiya da al’umma da kuma sauran masu ruwa da tsaki domin inganta ayyukan rigakafi da kuma tabbatar da cewa an dakile asarar rayuka da dukiyoyi a yayin wannan yanayi mai hatsari.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)