Katsina

Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin ÆŠan Bindiga, Abubakar Abba.

‎Gwamnatin Raɗɗa ta kashe Miliyan 700 kan sayen Litattafai a Makarantun jihar Katsina

‎

‎ Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa, gwamnatin sa ta kashe kuɗi kimanin Naira Miliyan 700 a kwanan baya, don siyan litattafai na makarantun Firamare da Sakandare da nufin farfaɗo da Al’adun karatu da kuma ƙarfafa bincike a tsakanin Ɗalibai a faɗin jihar.

‎

‎

‎Dikko Raɗɗa, ya bayyana haka ne a yayin da yake karɓar baƙuncin Babban Jami’ar kula da ɗakin karatu na ƙasa, Farfesa Chinwe Veronica, wadda ta kai masa ziyarar ban girma a gidan Gwamnati dake Katsina.

‎

‎

‎Hakan na ƙunshe ne a wata takarda da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a ranar Litinin 1 ga watan Satumba 2025, ya kuma rabawa Manema Labarai.

‎

‎

‎ ta samu cewa, Gwamnan ya lura da cewa, zuwan fasahohi da yawa na zamani dake a yanar Gizo, sun durƙusar da al’adar karatun ɗalibai da suke yi da juna tare, da kuma rage zurfin bincike tsakanin ɗalibai da ma Malamai, waɗanda a yanzu suka dogara da yanar gizo wajen gudanar da ayyukan ilimi.

‎

‎

‎

‎Ya ƙara nuni da cewa, yadda ake samun ƙaruwar amfani AI ayyukan ilimi, wanda ya ce yanzu ana amfani da su wajen shirya jawabai ga ayyukan ɗalibai, a wani ɓangare na kalubalen da ke fuskantar ci gaban ilimi mai ma’ana.

‎

‎

‎

‎Tunda farko, Gwamna Radda ya yabawa hukumar dakunan karatu ta ƙasa, bi sa zabar Katsina a matsayin mai masaukin baƙi kan taron shekara-shekara karo na 9, ya kuma tabbatar wa Farfesa Veronica cikakken goyon bayan gwamnatinsa don samun nasarar karɓar baƙuncin ta.

‎

‎

‎

‎Da take jawabi lokacin, shugabar ɗakin karatu ta ƙasa, Farfesa Chinwe Veronica, ta ce ta je Katsina ne domin halartar taron shekara shekara na cibiyar wanda shi ne karo na 9. Ta kuma bayyana godiya ga gwamnatin jihar Katsina bi sa goyon bayan da ta bayar wajen samun nasarar gudanar da taron.

‎

‎

‎

‎Farfesa Veronica ta ci gaba da yin kira da a ƙara haɗa kai da haɗin gwiwa wajen bunƙasa ilimin karatu da kuma farfado da al'adar karatun ɗalibai a rukunin bai ɗaya, ba a jihar Katsina kaɗai ba har ma a fadin ƙasar baki ɗaya.

‎

‎

‎

‎Ta kuma jaddada cewa, ɗakunan karatu na da matuƙar muhimmanci kan gina ɗaliban ƙasa, inda ta jaddada cewa samun ingantattun litattafai da kayan bincike za su baiwa Matasa ilimi da ƙirƙire-ƙirƙire da ake bukata don bayar da gudunmawa ga al'umma.

‎

‎


Comment As:

Comment (0)