
Shugaba Tinubu ya janye mukamin DG NTA da ya bai wa dan kudancin Nijeriya, ya dawo da dan Arewa mukaminsa
Shugaba Tinubu ya janye mukamin DG NTA da ya bai wa dan kudancin Nijeriya, ya dawo da dan Arewa mukaminsaÂ
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a dawo da Malam Salihu Abdullahi Dembos, Darakta Janar na gidan talabijin na kasar (NTA), yan kwanaki bayan da aka sauke Dembos din daga mukaminsa.
An naɗa Dembos a matsayin Darakta Janar na gidan talabijin ɗin a watan Oktoban 2023. Yanzu zai koma ya kammala wa’adin aikinsa na shekaru uku.
Haka kuma sanarwar da DCL Hausa ta samu daga fadar shugaban Nijeriya ta ce Tinubu ya dawo da Mista Ayo Adewuyi, Darakta mai kula da sashen Labarai, domin ya kammala wa’adin aikinsa na shekaru uku da zai ƙare a shekarar 2027.
Wannan sabon umarni ya soke nadin da aka sanar a baya na sabon Darakta Janar da sauran wasu daraktoci, dukkansu an soke nadin da aka yi musu.
Nagarifmradio