Shugaba kasa Tinubu ya tafi hutun sa na shekara- shekara zuwa Turai

Shugaba Tinubu ya tafi hutun sa na shekara- shekara zuwa Turai

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja yau Alhamis domin fara hutun sa na shekara-shekara na 2025.

Sanarwar fadar shugaban kasa ta ce shugaban zai yi hutun ne a Turai, inda zai shafe kwanaki goma na aiki.

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, ya ce Tinubu zai kwashe lokacin ne a Faransa da Birtaniya kafin dawowarsa gida Najeriya.

Hutun na bana dai shi ne na shekara ga shugaban, kuma ana sa ran zai dawo Najeriya bayan ya kammala hutun nasa a makonni biyu masu zuwa.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)